Markus 10:17-31
17
Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?”
18
Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.
19
Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’”
20
Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.”
21
Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”
22
Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.
23
Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!”
24
Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “’Ya’yana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah!
25
Ya fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”
26
Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?”
27
Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.”
28
Bitrus ya ce, “Mun bar kome domin mu bi ka!”
29
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara,
30
sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami.
31
Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma, za su zama na farko.”
Settings