Luka 9:9-14
9
Amma Hiridus ya ce, “Yohanna dai na yanke kansa, amma wanne mutum ne nake jin labarin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ƙoƙari ya ga Yesu.
10
Da manzannin suka dawo, sai suka faɗa wa Yesu abin da suka yi. Sai ya ɗauke su, suka keɓe kansu su kaɗai, zuwa wani gari da ake kira Betsaida.
11
Amma taron mutane suka ji labari, sai suka bi shi. Ya marabce su, kuma ya yi musu magana a kan mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkarwa.
12
Da rana ta kusa fāɗuwa, sai Sha Biyun suka zo wurinsa, suka ce, “Ka sallami taron domin su shiga ƙauyuka na kewaye, su nemi abin da za su ci, da wurin kwana, don inda muke, ba kowa.”
13
Yesu ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Sai suka ce masa, “Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron.”
14
Maza kaɗai sun kai kusan dubu biyar. Amma ya ce wa almajiransa, “Ku sa su su zauna a ƙungiya hamsin-hamsin.”
Settings