Skip to content
Luka 7:1-24

Luka 7:1-24

1
Bayan Yesu ya gama gaya wa mutanen dukan waɗannan abubuwa, sai ya shiga Kafarnahum.
2
A can, akwai wani bawan wani jarumin yana ciwo, yana kuma a bakin mutuwa. Maigidansa kuwa yana sonsa sosai.
3
Jarumin sojan ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu dattawan Yahudawa wajensa, yana roƙonsa yă zo yă warkar da bawansa.
4
Da suka isa wurin Yesu, sai suka roƙe shi sosai, suka ce, “Wannan mutum, ai, ya dace a yi masa haka,
5
gama yana ƙaunar al’ummarmu ta Yahudawa, har ya gina majami’armu.”
6
Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa, “Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba.
7
Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba. Amma ka yi magana kawai, bawana zai warke.
8
Gama ni kaina, mutum ne a ƙarƙashin iko, akwai kuma sojoji a ƙarƙashin ikona. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi, ga wani kuma in ce, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan kuma ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yă yi.”
9
Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake bin sa, “Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Isra’ila ba.”
10
Sai mutanen da aka aika, suka koma gida, suka tarar bawan ya warke.
11
Ba a daɗe ba, sai Yesu ya tafi wani garin da ake kira Nayin. Almajiransa da taro mai yawa suka tafi tare da shi.
12
Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita.
13
Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta ya ce, “Kada ki yi kuka.”
14
Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, “Saurayi, na ce maka, tashi!”
15
Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa.
16
Sai tsoro ya kama su duka, suka yabi Allah, suna cewa, “Babban annabi ya bayyana a cikinmu. Allah ya zo domin yă taimaki mutanensa.”
17
Wannan labarin game da Yesu, ya bazu ko’ina a Yahudiya da kewayenta.
18
Almajiran Yohanna suka gaya masa dukan waɗannan abubuwa. Sai ya kira biyu daga cikinsu,
19
ya aike su wurin Ubangiji, su tambaya su ce, “Kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?”
20
Da mutanen suka iso wurin Yesu, sai suka ce, “Yohanna Mai Baftisma ne ya aike mu wurinka, mu yi tambaya, ‘Ko kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?’ ”
21
A daidai lokacin nan, Yesu ya warkar da mutane da yawa masu ciwo, masu cututtuka, da kuma masu mugayen ruhohi. Ya kuma ba makafi da yawa ganin gari.
22
Sai ya amsa wa almajiran Yohanna ya ce, “Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka ji, da abin da kuka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin bishara.
23
Mai albarka ne mutumin da bai yi shakkar bangaskiyar da yake da ita a kaina ba.”
24
Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna ya ce, “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne?
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options