Aller au contenu
Luka 3:21-38

Luka 3:21-38

21
Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe,
22
Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”
23
To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa sa’ad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne, ɗan Heli,
24
ɗan Mattat, ɗan Lawi, ɗan Melki, ɗan Yannai, ɗan Yusuf,
25
ɗan Mattatiyas, ɗan Amos, ɗan Nahum, ɗan Esli, ɗan Naggai,
26
ɗan Ma’at, ɗan Mattatiyas, ɗan Semeyin, ɗan Yosek, ɗan Yoda,
27
ɗan Yowanan, ɗan Resa, ɗan Zerubbabel, ɗan Sheyaltiyel, ɗan Neri,
28
ɗan Melki, ɗan Addi, ɗan Kosam, ɗan Elmadam, ɗan Er,
29
ɗan Yoshuwa, ɗan Eliyezer, ɗan Yorim, ɗan Mattat, ɗan Lawi,
30
ɗan Simeyon, ɗan Yahuda, ɗan Yusuf, ɗan Yonam, ɗan Eliyakim,
31
ɗan Meleya, ɗan Menna, ɗan Mattata, ɗan Natan, ɗan Dawuda,
32
ɗan Yesse, ɗan Obed, ɗan Bowaz, ɗan Salmon, ɗan Nashon,
33
ɗan Amminadab, ɗan Ram, ɗan Hezron, ɗan Ferez, ɗan Yahuda,
34
ɗan Yaƙub, ɗan Ishaku, ɗan Ibrahim, ɗan Tera, ɗan Nahor,
35
ɗan Serug, ɗan Reyu, ɗan Feleg, ɗan Eber, ɗan Sala,
36
ɗan Kainan, ɗan Arfakshad, ɗan Shem, ɗan Nuhu, ɗan Lamek,
37
ɗan Metusela, ɗan Enok, ɗan Yared, ɗan Mahalalel, ɗan Kainan,
38
ɗan Enosh, ɗan Shitu, ɗan Adamu, ɗan Allah.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options