Luka 3:15-20
15
Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa.
16
Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma.
17
Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
18
Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara.
19
Amma da Yohanna ya tsawata wa Hiridus mai mulki saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa, da kuma dukan sauran mugayen abubuwan da ya yi,
20
Hiridus dai ya ƙara ɓata al’amarin. Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku.
Settings