Luka 23:20-25
20
Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu.
21
Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”
22
Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, sa’an nan in sāke shi.”
23
Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi.
24
Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu.
25
Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda tā da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Sa’an nan ya ba da Yesu ga nufinsu.
Settings