Skip to content
Luka 22:56-71

Luka 22:56-71

56
Wata baiwa ta gan shi zaune kusa da wutar. Ta dube shi sosai sa’an nan, ta ce, “Ai, wannan mutum ma yana tare da shi.”
57
Amma ya yi mūsu ya ce, “Mace, ban san shi ba!”
58
Bayan ɗan lokaci kaɗan, wani dabam ya gan shi ya ce, “Kai ma ɗayansu ne.” Bitrus ya amsa ya ce, “Kai, ba na cikinsu!”
59
Bayan kamar sa’a ɗaya, sai wani mutum ya ce, “Ba shakka, mutumin nan ma yana tare da shi, don shi mutumin Galili ne.”
60
Bitrus ya amsa ya ce, “Kai, ban ma san abin da kake magana a kai ba!” Yana cikin magana, sai zakara ya yi cara.
61
Ubangiji kuma ya juya ya kafa wa Bitrus ido. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Ubangiji ya ce masa, “Kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
62
Sai ya fita waje, ya yi kuka mai zafi.
63
Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa ba’a da dūka.
64
Suka rufe masa idanu suna tambaya cewa, “Ka yi annabci! Wa ya mare ka?”
65
Suka kuma yi masa waɗansu baƙaƙen maganganu masu yawa.
66
Da gari ya waye, sai majalisar dattawa na mutane, da manyan firistoci, da malaman dokoki, suka taru wuri ɗaya. Sai aka kawo Yesu a gabansu.
67
Suka ce, “Ka faɗa mana, ko kai ne Kiristi?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ni ba,
68
in kuma na yi muku tambaya ba za ku iya ba ni amsa ba.
69
Amma daga yanzu, Ɗan Mutum zai zauna a hannun dama na Allah Mai Iko.”
70
Sai dukansu suka yi tambaya suka ce, “Wato, kai Ɗan Allah ke nan?” Ya amsa ya ce, “Kun faɗa daidai, ni ne.”
71
Sai suka ce, “Wace shaida kuma muke nema? Ai, mun ji abin da ya ce da bakinsa.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options