Luka 11:42-52
42
“Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na na’ana’arku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon.
43
“Kaitonku, Farisiyawa, domin kun cika son wuraren zama masu daraja a majami’u, da kuma yawan gaisuwa a wuraren kasuwanci.
44
“Kaitonku, domin ku kamar kaburbura ne da ba a sa musu alama ba, waɗanda mutane suke takawa don rashin sani.”
45
Sai ɗaya daga cikin masanan dokoki ya ce wa Yesu, “Malam, in ka faɗi waɗannan abubuwa haka, kai kuma ka zage mu ke nan.”
46
Yesu ya amsa ya ce, “Ku masanan dokoki ma, kaitonku, domin kun ɗora wa mutane kaya masu nauyi waɗanda da ƙyar suke ɗaukawa, amma ku da kanku ba za ku sa ko yatsa ɗaya, don ku taimake su ba.
47
“Kaitonku, domin kun gina kaburbura saboda annabawa, nan kuwa kakannin-kakanninku ne suka kashe su.
48
Wannan ya shaida cewa kun amince da abin da kakannin-kakanninku suka yi. Sun karkashe annabawa, ku kuma kun gina kaburburansu.
49
Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’
50
Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani,
51
wato, tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagade da mazauni. I, ina gaya muku, alhakinsu duka yana kan wannan zamani.
52
“Kaitonku, masanan dokoki, domin kun ɗauke mabuɗin ilimi. Ku kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana wa waɗanda suke shiga, su shiga.”
Settings