Firistoci 25:35-40
35
“ ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku.
36
Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku.
37
Kada ku ba shi rancen kuɗi da ruwa, ko ku sayar masa abinci don samun riba.
38
Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, don in ba ku ƙasar Kan’ana in kuma zama Allahnku.
39
“ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta a cikinku, ya kuma sayar da kansa gare ku, kada ku sa yă yi kamar bawa.
40
Amma a ɗauke shi a matsayin ma’aikacin da aka ɗauka aiki, ko mazaunan da ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, sai yă yi muku aiki sai Shekara ta Murna.
Settings