Mahukunta 7:16-25
16
Ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho da tulu da acibalbal a ciki.
17
Ya ce musu, “Ku dube ni, ku bi abin da na yi. Sa’ad da na kai sansanin, ku yi daidai abin da na yi.
18
Sa’ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoninmu, to, ko’ina a kewayen sansanin sai ku busa naku ku kuma yi ihu, ku ce, ‘Don Ubangiji da kuma domin Gideyon.’ ”
19
Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu.
20
Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka ɗauki acibalbal a hannuwansu na hagu da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama, sai suka yi ihu, “Takobi don Ubangiji da kuma don Gideyon!”
21
Yayinda kowannensu ya tsaya a inda yake kewaye da sansanin, dukan Midiyawa suka fito da gudu, suna kuka yayinda suke gudu.
22
Sa’ad da aka busa ƙahonin nan ɗari uku sai Ubangiji ya sa Midiyawa suka yi ta saran juna. Mayaƙan suka gudu zuwa Bet-Shitta wajen Zerera har zuwa yankin Abel-Mehola kusa da Tabbat.
23
Aka kira dukan Isra’ilawa daga Naftali, Asher da dukan Manasse, suka kuwa fatattaki Midiyawa.
24
Gideyon ya aiki manzanni zuwa dukan ƙasar tudu ta Efraim cewa, “Ku gangaro ku yaƙi Midiyawa ku ƙwace ruwan Urdun gaba da su har zuwa Bet-Bara.” Saboda haka aka kira dukan mutanen Efraim suka ƙwace ruwan Urdun har zuwa Bet-Bara.
25
Suka kuma kama shugabannin biyu na Midiyawa, Oreb da Zeyib suka kashe Oreb a dutsen Oreb, Zeyib kuma a wurin matsin ruwa inabin Zeyib. Suka fatattaki Midiyawa suka kawo kawunan Oreb da Zeba wurin Gideyon, wanda yake kusa da Urdun.
Settings