Skip to content
Mahukunta 19:12-16

Mahukunta 19:12-16

12
Maigidansa ya ce, “A’a. Ba za mu shiga birnin baƙi waɗanda mutanensu ba Isra’ilawa ba. Za mu ci gaba zuwa Gibeya.”
13
Ya kuma ce, “Zo, mu yi ƙoƙari mu kai Gibeya ko Rama mu kwana a ɗaya cikinsu.”
14
Saboda haka suka ci gaba, rana tana fāɗuwa sa’ad da suka yi kusa da Gibeya a Benyamin.
15
A can suka dakata don su kwana, suka tafi suka zauna a dandali birnin, amma wani ya shigar da su gidansa da daren.
16
A wannan yamma sai ga wani tsoho daga ƙasar tudu ta Efraim, wanda yake zama a Gibeya (mutane wurin kuwa mutanen Benyamin ne), ya shigo daga wurin aiki a gonaki.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options