Skip to content
Mahukunta 15:9-19

Mahukunta 15:9-19

9
Filistiyawa suka haura suka yi sansani a Yahuda, suka bazu kusa da Lehi.
10
Mutanen Yahuda suka ce, “Me ya sa kuka zo mana da yaƙi?” Sai suka ce, “Mun zo ne mu kama Samson, a matsayin fursunan yaƙi, mu yi masa kamar yadda ya yi mana.”
11
Sa’an nan mutane dubu uku daga Yahuda suka gangara wajen Samson a kogo a dutsen Etam. Suka ce masa, “Ba ka san cewa Filistiyawa ne suke mulkinmu ba? Me ke nan ka yi mana?” Ya ce musu, “Na ɗan yi musu abin da suka yi mini ne.”
12
Suka ce masa, “To, mun zo ne mu daure ka mu kai wa Filistiyawa.” Samson ya ce, “Ku rantse mini ba za ku kashe ni da kanku ba.”
13
Suka ce, “Mun yarda, za mu dai daure ka mu ba da kai gare su. Ba za mu kashe ka ba.” Saboda haka suka daure shi da sababbin igiyoyi biyu, suka saukar da shi daga dutsen.
14
Yayinda ya zo gab da Lehi, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje da ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko da iko a kansa. Igiyoyin da suke daure a hannuwansa kuwa suka zama kamar abin da wuta ta babbaka, suka tsintsinke suka zuba daga hannuwansa.
15
Da ya samo muƙamuƙin jaki, ya ɗauka, sai ya karkashe mutane dubu ɗaya.
16
Sa’an nan Samson ya ce, “Da muƙamuƙin jaki na mai da su jakuna. Da muƙamuƙin jaki na kashe mutum dubu.”
17
Da ya gama magana, sai ya jefar da muƙamuƙin; aka ba wa wannan wuri suna Ramat Lehi.
18
Saboda ƙishirwa ta kama shi ƙwarai, sai ya ce wa Ubangiji, “Ka ba bawanka wannan babbar nasara. To, sai in mutu da ƙishirwa, har in shiga a hannun marasa kaciyan nan su kashe ni?”
19
Sa’an nan Allah ya buɗe wani rami a Lehi, ruwa kuwa ya fito daga ciki. Da Samson ya sha, sai ƙarfinsa ya dawo, ya kuma wartsake. Aka sa wa wannan maɓulɓula suna En Hakkore, yana nan a Lehi har wa yau.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options