Skip to content
Mahukunta 11:34-40

Mahukunta 11:34-40

34
Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi, ’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai ’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko ’ya.
35
Da ya gan ta, sai ya yayyage tufafinsa ya yi kuka ya ce, “Kaito! ’Yata! Kin karya mini gwiwa, kuma na lalace, domin na yi wa’adi ga Ubangiji da ba zan iya in karya ba.”
36
Ta ce, “Mahaifina, idan ka riga ka yi wa Ubangiji magana, sai ka yi da ni yadda ka yi alkawari, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa.”
37
Sai ta kuma ce, “Sai dai, ka biya mini wannan bukata guda. Ka ba ni wata biyu in yi ta yawo da ni da ƙawayena a kan duwatsu mu yi makoki, domin ba zan yi aure ba.”
38
Ya ce mata, “Ki tafi,” Ya bar ta tă tafi har wata biyu. Ita da ’yan matan suka tafi a kan duwatsu suka yi ta makoki domin ba za tă taɓa aure ba.
39
Bayan watanni biyu ɗin sai ta komo wurin mahaifinta ya kuwa yi da ita yadda ya yi wa’adi. Ita kuwa ba tă taɓa san namiji ba. Wannan ya zama al’ada a Isra’ila,
40
cewa kowace shekara ’yan mata sukan fita kwana huɗu don yin bikin tunawa da ’yar Yefta mutumin Gileyad.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options