Yoshuwa 9:15-27
15
Sa’an nan Yoshuwa ya yi alkawari zaman salama da su, cewa ba zai kashe su ba, sai shugabannin mutanen Isra’ila kuwa suka tabbatar musu da haka ta wurin yin rantsuwa.
16
Kwana uku bayan sun yi alkawari da Gibeyonawa, sai Isra’ilawa suka ji cewa Gibeyonawa maƙwabtansu ne, waɗanda suke zaune kurkusa da su.
17
Saboda haka Isra’ilawa suka tashi a rana ta uku suke je biranen mutanen, wato, Gibeyon, Kefira, Beyerot da Kiriyat Yeyarim.
18
Amma Isra’ilawa ba su kai musu hari ba domin shugabanninsu sun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Mutane Isra’ila duka kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin.
19
Amma shugabanni suka amsa musu suka ce, “Mun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, saboda haka ba za mu taɓa su ba yanzu.
20
Ga abin da za mu yi musu, za mu bar su da rai don kada fushin Allah yă sauka a kanmu gama mun riga mun rantse musu.”
21
Suka ƙara da cewa, “Mu bar su da rai, amma bari su zama masu yankan itace da masu ɗibo mana ruwa.” Haka shugabannin suka cika alkawarinsu.
22
Yoshuwa kuwa ya aika aka kira Gibeyonawa ya ce musu, “Don me kuka ruɗe mu kuka ce, ‘Mun zo ne daga wuri mai nisa,’ bayan kuwa kuna nan kurkusa da mu?
23
Yanzu ku la’anannu ne. Ba za ku daina zama mana masu yankan itace da kuma masu ɗebo ruwa domin haikalin Allahnmu ba.”
24
Suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “An gaya wa bayinka dalla-dalla yadda Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa yă ba ka ƙasar duka, ka kuma kashe duk masu zama a cikinta, muka ji tsoro cewa za ka kashe mu shi ya sa muka yi haka.
25
Yanzu, a hannunka muke, ka yi duk abin da ka ga ya yi maka kyau.”
26
Yoshuwa kuwa ya cece su daga hannun Isra’ilawa, har ba su kashe su ba.
27
A ranar Yoshuwa ya sa Gibeyonawa suka zama masu yankan itace da ɗebo ruwa wa jama’ar Isra’ila da kuma domin haikalin Ubangiji a inda Ubangiji zai zaɓa. Abin da suke ke nan har wa yau.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings