Skip to content
Yoshuwa 6:1-16

Yoshuwa 6:1-16

1
Ƙofofin Yeriko kuwa a kulle suke ciki da waje saboda Isra’ilawa, ba mai fita babu kuma mai shiga.
2
Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Duba, na ba ka nasara a kan Yeriko, duk da sarkinta da mayaƙanta.
3
Da kai da dukan sojoji, ku zaga birnin sau ɗaya kullum. Ku yi haka har kwana shida.
4
Ka sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni raguna su kasance a gaban akwatin alkawari. A rana ta bakwai sai ku zaga birnin sau bakwai, firistocin suna busa ƙahoni.
5
Sa’ad da kuka ji sun ɗauki dogon lokaci suna busa ƙaho, sai mutane gaba ɗaya su tā da murya su yi ihu da ƙarfi; katangar birnin kuwa za tă rushe, sai sojoji su haura, ko wanne yă nufi inda ya fuskanta kai tsaye.”
6
Yoshuwa ɗan Nun kuwa ya kira firistoci ya ce musu, “Ku ɗauki akwatin alkawari, ku sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni su kasance a gabansa.”
7
Sai ya umarci jama’a ya ce, “Mu je zuwa! Ku zaga birnin, masu tsaro da makamai su shiga gaban akwatin alkawarin Ubangiji.”
8
Da Yoshuwa ya gama yin wa mutane magana, sai firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai a gaban Ubangiji suka sha gaba suna busa ƙahoninsu, akwatin alkawari kuwa yana biye da su.
9
Masu tsaro da makamai kuma suna gaban firistoci waɗanda suke busa ƙahoni, masu tsaro daga baya kuma suna bin akwatin alkawari, ana ta busa ƙahoni.
10
Amma Yoshuwa ya umarci mutane ya ce, “Kada ku yi kururuwar yaƙi, kada ku tā da murya, kada ku ce kome, sai ranar da na ce ku yi ihu, a sa’an nan ne sai ku yi ihu!”
11
Sai ya sa aka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji aka kewaye birnin da shi sau ɗaya, sa’an nan mutane suka dawo masauƙinsu suka kwana a can.
12
Kashegari, Yoshuwa ya tashi da sassafe, firistoci kuma suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji.
13
Firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai suka shiga gaba, suna takawa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji suna kuma busa ƙahoni, masu tsaro ɗauke da makamai suna gabansu, sai masu tsaro da suke baya suna biye da akwatin alkawarin Ubangiji.
14
A rana ta biyu suka sāke zaga birnin sau ɗaya, suka kuma koma masauƙinsu. Haka suka yi har kwana shida.
15
A rana ta bakwai, suka tashi da sassafe suka zaga birnin sau bakwai yadda suka saba. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai.
16
A zagawa ta bakwai, da firistoci suka busa ƙahoni, sai Yoshuwa ya ba sojojin umarni ya ce, “Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin!
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options