Yoshuwa 6:6-14
6
Yoshuwa ɗan Nun kuwa ya kira firistoci ya ce musu, “Ku ɗauki akwatin alkawari, ku sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni su kasance a gabansa.”
7
Sai ya umarci jama’a ya ce, “Mu je zuwa! Ku zaga birnin, masu tsaro da makamai su shiga gaban akwatin alkawarin Ubangiji.”
8
Da Yoshuwa ya gama yin wa mutane magana, sai firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai a gaban Ubangiji suka sha gaba suna busa ƙahoninsu, akwatin alkawari kuwa yana biye da su.
9
Masu tsaro da makamai kuma suna gaban firistoci waɗanda suke busa ƙahoni, masu tsaro daga baya kuma suna bin akwatin alkawari, ana ta busa ƙahoni.
10
Amma Yoshuwa ya umarci mutane ya ce, “Kada ku yi kururuwar yaƙi, kada ku tā da murya, kada ku ce kome, sai ranar da na ce ku yi ihu, a sa’an nan ne sai ku yi ihu!”
11
Sai ya sa aka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji aka kewaye birnin da shi sau ɗaya, sa’an nan mutane suka dawo masauƙinsu suka kwana a can.
12
Kashegari, Yoshuwa ya tashi da sassafe, firistoci kuma suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji.
13
Firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai suka shiga gaba, suna takawa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji suna kuma busa ƙahoni, masu tsaro ɗauke da makamai suna gabansu, sai masu tsaro da suke baya suna biye da akwatin alkawarin Ubangiji.
14
A rana ta biyu suka sāke zaga birnin sau ɗaya, suka kuma koma masauƙinsu. Haka suka yi har kwana shida.
Settings