Yoshuwa 20:2-6
2
“Ka gaya wa Isra’ilawa su keɓe waɗansu birane su zama biranen mafaka kamar yadda na umarce ku ta wurin Musa,
3
domin idan wani ya kashe wani bisa kuskure ba da niyyar yin kisankai ba, mutumin zai iya gudu zuwa can yă fake don kada a kashe shi.
4
Lokacin da ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen nan, sai yă tsaya a ƙofar birnin yă gaya wa dattawan wannan birni damuwarsa. Sa’an nan su karɓe shi su ba shi wurin zama a cikin birninsu.
5
In mai neman yă kashe shi don ramako ya bi shi zuwa can, ba za su miƙa shi ba domin ba da niyya ya kashe wani ba, kuma ba fushi ne ya sa ya yi kisan ba.
6
Zai zauna a wannan birni har sai taron jama’a sun yi masa shari’a, kuma har sai lokacin da babban firist wanda yake aiki a lokacin ya mutu, sa’an nan zai iya koma garinsa na dā.”
Settings