Skip to content
Yoshuwa 16:1-4

Yoshuwa 16:1-4

1
Rabon da aka ba wa Yusuf ya fara tun daga Urdun kusa da Yeriko, gabas da ruwan Yeriko, sai ya miƙe zuwa jeji, ya haura har zuwa cikin ƙasar tudu na Betel.
2
Ya ci gaba daga Betel (wato, Luz), ya zarce zuwa sashen Arkitawa na Atarot,
3
ya sauka zuwa yammancin bakin iyakar Yalfetiyawa har zuwa yankin Bet-Horon wanda yake cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, ya gangara ya yi ƙarshe a Bahar Rum.
4
Wannan ne yankin da aka ba wa Manasse da Efraim zuriyar Yusuf gādonsu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options