Rashin Fitar da Yebusiyawa
Ana nuna aya 63 tare da mahallin da ke kewaye.
60
Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim) da Rabba, garuruwa biyu ke nan da ƙauyukansu.
61
Biranen da suke a jeji kuwa su ne, Bet-Araba, Middin, Sekaka,
62
Nibshan, Birnin gishiri da En Gedi, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu.
63
Kabilar Yahuda kuwa ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zama cikin Urushalima ba; har wa yau Yebusiyawa suna nan zaune tare da mutanen Yahuda.
Settings