Skip to content
Yoshuwa 11:8-15

Yoshuwa 11:8-15

8
Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa nasara a kan su, suka ci su da yaƙi, suka fafare su har zuwa Sidon Babba, zuwa Misrefot Mayim, har zuwa Kwarin Mizfa a gabas, ba wanda suka bari da rai.
9
Yoshuwa ya yi musu yadda Ubangiji ya umarta, ya gurgunta dawakansu, ya kuma ƙone keken yaƙinsu.
10
A lokacin nan Yoshuwa ya koma da baya ya ci Hazor da yaƙi, ya kuma kashe sarkinta da takobi. (Hazor ce babbar masarautan ƙasashen nan.)
11
Suka karkashe duk mazaunan ƙasar da takobi, ba su bar wani mai numfashi ba, suka kuma ƙona Hazor.
12
Yoshuwa ya ƙwace masarautun nan duka ya kuma kashe sarakunansu da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta.
13
Duk da haka Isra’ilawa ba su ƙone biranen da suke kan tuddai ba, sai Hazor kaɗai Yoshuwa ya ƙone.
14
Isra’ilawa suka kwashi ganima da dabbobi na waɗannan birane, amma suka karkashe mutanen duka da takobi, ba su bar wani mai numfashi ba.
15
Yadda Ubangiji ya umarci bawansa Musa, haka Musa ya umarci Yoshuwa, shi kuwa ya yi duk abin da Ubangiji ya umarci Musa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options