Yohanna 7:32-49
32
Farisiyawa suka ji taron suna raɗe-raɗen waɗannan abubuwa game da shi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki masu gadin haikalin su kama shi.
33
Sai Yesu ya ce, “Ina tare da ku na ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai, sa’an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni.
34
Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba; inda nake kuwa, ba za ku iya zuwa ba.”
35
Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina mutumin nan yake niyyar tafiya da ba za mu iya samunsa ba? Zai je wurin mutanenmu da suke zaune warwatse a cikin Hellenawa, yă kuma koya wa Hellenawa ne?
36
Me yake nufi da ya ce, ‘Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba,’ da kuma ‘Inda nake, ba za ku iya zuwa ba’?”
37
A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yă zo wurina yă sha.
38
Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.”
39
Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.
40
Da jin kalmominsa, waɗansu mutane suka ce, “Ba shakka, mutumin nan shi ne Annabin.”
41
Waɗansu suka ce, “Shi ne Kiristi.” Waɗansu har wa yau suka ce, “Yaya Kiristi zai fito daga Galili?
42
Nassi bai ce Kiristi zai fito daga zuriyar Dawuda, daga kuma Betlehem garin da Dawuda ya zauna ba?”
43
Sai mutanen suka rabu saboda Yesu.
44
Waɗansu suka so su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi.
45
A ƙarshe masu gadin haikali suka koma wurin manyan firistocin da Farisiyawa, waɗanda suka tambaye su cewa, “Don me ba ku kawo shi nan ba?”
46
Sai masu gadin suka ce, “Kai, babu wanda ya taɓa magana kamar wannan mutum.”
47
Sai Farisiyawa suka amsa cikin fushi suka ce, “Af, kuna nufi har da ku ma ya ruɗe ku ke nan?
48
Akwai wani daga cikin masu mulki ko cikin Farisiyawan da ya gaskata da shi?
49
A’a! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba, la’anannu ne.”
Settings