Skip to content
Yohanna 4:6-26

Yohanna 4:6-26

6
Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen sa’a ta shida ne.
7
Sa’ad da wata mutuniyar Samariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha?”
8
(Almajiransa kuwa sun shiga gari don sayi abinci.)
9
Sai mutuniyar Samariyar ta ce masa, “Kai mutumin Yahuda ne, ni kuwa mutuniyar Samariya ce. Yaya za ka roƙe ni ruwan sha?” (Don Yahudawa ba sa hulɗa da Samariyawa.)
10
Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, shi kuwa da ya ba ki ruwan rai.”
11
Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ba ka da guga rijiyar kuwa tana da zurfi. Ina za ka sami wannan ruwan rai?
12
Ka fi mahaifinmu Yaƙub ne, wanda ya ba mu rijiyar ya kuma sha daga ciki da kansa, haka ma ’ya’yansa da kuma garkunan shanunsa da tumakinsa?”
13
Yesu ya amsa ya ce, “Kowa ya sha wannan ruwa, zai sāke jin ƙishirwa,
14
amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.”
15
Sai macen ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, in yi ta zuwa nan ɗiban ruwa.”
16
Sai ya ce mata, “Je ki zo da mijinki.”
17
Sai ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji.
18
Gaskiyar ita ce, kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.”
19
Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ina gani kai annabi ne.
20
Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan, amma ku Yahudawa kun ce a Urushalima ne ya kamata a yi sujada.”
21
Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba.
22
Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake.
23
Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.
24
Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”
25
Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu” (da ake ce da shi Kiristi) “yana zuwa. Sa’ad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.”
26
Sai Yesu ya ce, “Ni mai maganan nan da ke, Ni ne shi.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options