Skip to content
Yohanna 19:1-16

Yohanna 19:1-16

1
Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala.
2
Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya.
3
Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.
4
Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.”
5
Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”
6
Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!” Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”
7
Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”
8
Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi,
9
sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba.
10
Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?”
11
Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”
12
Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”
13
Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata).
14
Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida. Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.”
15
Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”
16
A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options