Skip to content
Ayuba 28:12-28

Ayuba 28:12-28

12
Amma a ina ne za a iya samun hikima? Ina fahimta take zama?
13
Mutum bai gane muhimmancinta ba, ba a samunta a ƙasar masu rai.
14
Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”; teku ya ce, “Ba ta wurina.”
15
Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta, ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.
16
Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba.
17
Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba, ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.
18
Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai.
19
Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba, zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba.
20
“To, daga ina ke nan hikima ta fito? Ina fahimta take zama?
21
An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai, har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita.
22
Hallaka da mutuwa suna cewa, ‘Jita-jitarta kaɗai muke ji.’
23
Allah ya gane hanyar zuwa wurinta. Shi ne kaɗai ya san inda take zama,
24
Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.
25
Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye.
26
Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka da kuma hanya domin walƙiya,
27
sai ya dubi hikima ya auna ta; ya tabbatar da ita, ya gwada ta.
28
Ya kuma ce wa mutum, ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima, kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options