Irmiya 43:10-13
10
Sa’an nan ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, zan aika wa bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon, zan kuma sa kursiyinsa a kan waɗannan duwatsun da na binne a nan; zai fadada bukkar mulkinsa a bisansu.
11
Zai zo ya yaƙi Masar, ya kawo mutuwa ga waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa, zaman bauta ga waɗanda aka ƙaddara musu zaman bauta, da kuma takobi ga waɗanda aka ƙaddara su mutu ta takobi.
12
Zai sa wuta wa haikalan allolin Masar; zai ƙone haikalansu yă kuma kwashe allolinsu bayi. Kamar yadda makiyayi yakan yafa mayafinsa kewaye da shi, haka zai yafa Masar kewaye da kansa ya kuma tashi a wurin babu abin da ya same shi.
13
A can cikin haikalin rana a Masar zai rushe al’amudan duwatsu yă kuma ƙone haikalan allolin Masar.’ ”
Settings