Irmiya 38:10-13
10
Sai sarki ya umarce Ebed-Melek mutumin Kush, “Ka ɗauko mutane talatin daga nan ku fid da Irmiya annabi daga rijiyar kafin ya mutu.”
11
Saboda haka Ebed-Melek ya ɗauki mutane tare da shi suka shiga ɗaki a ƙarƙashin baitulmali a cikin fada. Ya ɗauko waɗansu tsofaffin tsummoki da tsofaffi riguna daga can ya kuma zurara su da igiya wa Irmiya a cikin rijiyar.
12
Ebed-Melek mutumin Kush ya ce wa Irmiya, “Ka sa waɗannan tsummoki da tsofaffin rigunan a hammatarka, ya zarga igiya.” Irmiya ya yi haka,
13
suka kuma ja shi sama da igiya suka fid da shi daga rijiyar. Irmiya kuwa ya zauna a sansanin matsara.
Settings