Skip to content
Irmiya 30:1-12

Irmiya 30:1-12

1
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.
2
“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ka rubuta a cikin littafi dukan maganganun da na yi maka.
3
Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan komo da mutanena Isra’ila da Yahuda daga bauta in kuma maido da su ga ƙasar da na ba wa kakanninsu mallaka,’ in ji Ubangiji.”
4
Ga kalmomin Ubangiji da ya yi game da Isra’ila da Yahuda,
5
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ana jin kukan tsoro, razana, ba salama ba.
6
Ku tambaya ku ji. Namiji zai iya haifi ’ya’ya? To, me ya sa kuke ganin kowane mai ƙarfi da hannuwansa a kwankwaso kamar mace mai naƙuda, kowace fuska ta koma fari?
7
Kaito, gama wannan rana za tă zama mai girma! Babu kamar ta. Zai zama lokacin wahala wa Yaƙub, amma za a cece shi daga cikinta.
8
“ ‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘Zan karya karkiya daga wuyansu zan kuma cire musu kangi; baƙi ba za su ƙara bautar da su ba.
9
A maimakon haka, za su bauta wa Ubangiji Allahnsu Dawuda sarkinsu kuwa, wanda na tayar musu.
10
“ ‘Saboda haka kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila,’ in ji Ubangiji. ‘Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nesa, zuriyarka daga ƙasar zaman bautansu. Yaƙub zai sami salama da zaman lafiya, kuma ba wanda zai sa ya ji tsoro.
11
Ina tare da kai zan kuma cece ka,’ in ji Ubangiji. ‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗaya a inda na warwatsa ku, ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Zan hore ku amma da adalci kaɗai; ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’
12
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Mikinku marar warkewa ne, raunin da kuka ji ya sha ƙarfin warkarwa.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options