Skip to content
Irmiya 2:20-28

Irmiya 2:20-28

20
“Tun da daɗewa ka karya karkiyarka ka kuma tsintsinke sarƙoƙinka; sai ka ce, ‘Ba zan bauta maka ba!’ Tabbatacce, a kan kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane ɗanyen itace ka kwanta kamar karuwa.
21
Na shuka ka kamar zaɓaɓɓen inabi iri mai kyau da kuma wanda za a dogara a kai. Yaya kuma ka juya kana gāba da ni ka lalace, ka zama inabin jeji?
22
Ko da yake ka wanke kanka da sabulu ka yi amfani da sabulu mai yawa, duk da haka har yanzu tabon laifinka yana nan a gabana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
23
“Yaya za ka ce, ‘Ban ƙazantu ba; ban bi Ba’al ba’? Duba yadda ka yi a cikin kwari; ka ga abin da ka yi. Kai kamar makwaɗaciyar raƙuma ce mai zafin gudu kana gudu nan da can,
24
kamar jakar jejin da ta saba da hamada, mai busar iska cikin son barbaranta sa’ad da take son barbara wa zai iya hana ta? Jakin da yake nemanta, ba ya bukatar wahalar da kansa; a lokacin barbara za a same ta.
25
Kada ka yi gudu har ƙafafunka su zama ba takalma maƙogwaronka kuma ya bushe. Amma sai ka ce, ‘Ba amfani! Ina ƙaunar baƙin alloli kuma dole in bi su.’
26
“Kamar yadda akan kunyatar da ɓarawo sa’ad da aka kama shi, haka gidan Isra’ila zai sha kunya, su, sarakunansu da shugabanninsu, firistocinsu da kuma annabawansu.
27
Kuna ce wa itace, ‘Kai ne mahaifina,’ ga dutse kuma, ‘Kai ne ka haife ni.’ Sun juye mini bayansu ba fuskokinsu ba; duk da haka sa’ad da suna cikin wahala, sukan ce, ‘Zo ka cece mu!’
28
To ina allolin da kuka yi wa kanku? Bari su zo in suna iya cetonku sa’ad da kuke cikin wahala! Gama kuna da alloli masu yawa kamar yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options