Skip to content
Irmiya 2:29-37

Irmiya 2:29-37

29
“Me ya sa kuke tuhumana? Dukanku kun yi mini tawaye,” in ji Ubangiji.
30
“A banza na hukunta mutanenku; ba su yi gyara ba. Takobinku ya cinye annabawanku kamar zaki mai jin yunwa.
31
“Ku na wannan zamani, ku saurari maganar Ubangiji. “Na zama wa Isra’ila hamada ne ko ƙasa mai babban duhu? Me ya sa mutanena suke cewa, ‘Muna da ’yanci mu yi ta yawo; ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?
32
Budurwa za tă manta da kayan adonta amarya ta manta da kayan adon aurenta? Duk da haka mutanena sun manta da ni, kwanaki ba iyaka.
33
Kuna da azanci sosai a bin masoya! Kai, ko mafiya muni cikin mata tana iya koya daga hanyoyinku.
34
A rigunanku mutane kan sami jinin matalauta marasa laifi, ko da yake ba ku kama su suna fasawa su shiga ba. Duk da haka
35
kuna cewa, ‘Ba ni da laifi; ba ya fushi da ni.’ Amma zan zartar da hukunci a kanku domin kun ce, ‘Ban yi zunubi ba.’
36
Don me kuke yawo da yawa haka, kuna ta canjin hanyoyinku? Masar za tă kunyata ku yadda kuka sha kunya a wurin Assuriya.
37
Za ku kuma bar wurin da hannuwanku a kanku, gama Ubangiji ya ƙi waɗanda kuka amince da su; ba za ku zama abin taimako a gare su ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options