跳到主要内容
Yaƙub 3:9-12

Yaƙub 3:9-12

9
Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke la’antar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah.
10
Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa. ’Yan’uwana, wannan bai kamata yă zama haka ba.
11
Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya?
12
’Yan’uwana, itacen ɓaure yana iya haifar ’ya’yan zaitun, ko kuma itacen inabi yă haifi ’ya’yan ɓaure? Haka ma, maɓulɓular ruwan gishiri ba zai iya ba da ruwa mai kyau ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options