Skip to content
Ishaya 5:1-15

Ishaya 5:1-15

1
Zan rera waƙa wa ƙaunataccena waƙa game da gonar inabinsa. Ƙaunataccena yana da gonar inabi a gefen tudu mai dausayi.
2
Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun ya shuka mata inabi mafi kyau. Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi. Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin, amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya.
3
“Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda, ku shari’anta tsakanina da gonar inabina.
4
Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina fiye da abin da na yi mata? Da na nemi inabi masu kyau, me ya sa ta ba da munana ’ya’ya?
5
Yanzu zan faɗa muku abin da zan yi da gonar inabina. Zan cire katangar da ta kewaye ta, za tă kuwa lalace; zan rushe bangonta, za a kuwa tattake ta.
6
Zan mai da ita kango, ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba, sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can Zan umarci gizagizai kada su yi ruwan sama a kanta.”
7
Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki ita ce gidan Isra’ila, mutanen Yahuda kuma su ne lambun farin cikinsa. Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini; yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.
8
Kaitonku ku waɗanda kuke ƙara wa kanku gidaje kuke kuma haɗa gonaki da gonaki har babu sauran filin da ya rage ku kuma zauna ku kaɗai a ƙasar.
9
Ubangiji Maɗaukaki ya furta a kunnuwana, “Tabbatacce manyan gidajen za su zama kango, za a bar kyawawan gidajen nan ba kowa.
10
Kadada goma na gonar inabi zai ba da garwan ruwan inabi ɗaya kaɗai, mudu guda na iri kuma zai ba da efa na hatsi guda kurum.”
11
Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe don su nufi wurin shaye-shaye, waɗanda suke raba dare har sai sun bugu da ruwan inabi.
12
Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu, ganguna da busa da ruwan inabi, amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba, ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.
13
Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta domin rashin fahimi; manyan mutanensu za su mutu da yunwa talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa.
14
Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka; cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu.
15
Ta haka za a ƙasƙantar da mutum kuma za a ƙasƙantar da ’yan adam, za a ƙasƙanta da masu girman kai.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options