Ishaya 38:9-20
9
Rubutun Hezekiya sarkin Yahuda bayan ciwonsa da kuma warkarwarsa.
10
Na ce, “Cikin tsakiyar rayuwata dole in bi ta ƙofofin mutuwa a kuma raba ni da sauran shekaruna?”
11
Na ce, “Ba zan ƙara ganin Ubangiji ba, Ubangiji a ƙasa ta masu rai; ba zan ƙara ga wani mutum, ko in kasance tare da waɗanda suke zama a wannan duniya ba.
12
Kamar tentin makiyayi an rushe gidana aka kuma ƙwace ta daga gare ni. Kamar mai saƙa, na nannaɗe rayuwata, ya kuma yanke ni daga sandar saƙa; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.
13
Na yi jira da haƙuri har safiya, amma kamar zaki ya kakkarya ƙasusuwana duka; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.
14
Na yi kuka kamar mashirare ko zalɓe, na yi kuka kamar kurciya mai makoki. Idanuna suka rasa ƙarfi yayinda na duba sammai. Na damu; Ya Ubangiji, ka taimake ni!”
15
Amma me zan ce? Ya riga ya yi mini magana, shi kansa ne kuma ya aikata. Zan yi tafiya da tawali’u dukan kwanakina saboda wahalar raina.
16
Ubangiji, ta waɗannan abubuwa ne mutane suke rayuwa; ruhuna kuma yana samun rai a cikinsu shi ma. Ka maido mini da lafiya ka kuma sa na rayu.
17
Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne cewa in sha irin wahalan nan. Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni daga ramin hallaka; ka sa dukan zunubaina a bayanka.
18
Gama kabari ba zai yabe ka ba, matattu ba za su rera yabonka ba; waɗanda suka gangara zuwa rami ba za su sa zuciya ga amincinka ba.
19
Masu rai, masu rai, su suke yabonka, kamar yadda nake yi a yau; iyaye za su faɗa wa ’ya’yansu game da amincinka.
20
Ubangiji zai cece ni, za mu kuma rera da kayan kiɗi masu tsirkiya dukan kwanakinmu a cikin haikalin Ubangiji.
Settings