Skip to content
Ishaya 38:1-8

Ishaya 38:1-8

1
A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da ciwo ya kuma kusa ya mutu. Annabi Ishaya ɗan Amoz ya tafi wurinsa ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce ka shirya gidanka, domin za ka mutu; ba za ka warke ba.”
2
Hezekiya ya juye fuskarsa wajen bango ya kuma yi addu’a ga Ubangiji,
3
“Ka tuna, ya Ubangiji, yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukan zuciya na kuma yi abin da yake nagari a idanunka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.
4
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Ishaya cewa,
5
“Ka tafi ka faɗa wa Hezekiya, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, ya ce na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan ƙara maka shekaru goma sha biyar ga rayuwarka.
6
Zan kuwa cece ka da wannan birni daga hannun sarkin Assuriya. Zan kiyaye wannan birni.
7
“ ‘Ga alamar Ubangiji gare ka cewa Ubangiji zai aikata kamar yadda ya yi alkawari.
8
Zan sa inuwar da rana ta yi a kan matakalar Ahaz ta koma baya da taki goma.’ ” Saboda haka inuwar ta koma da baya daga fuskar rana har taki goma.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options