Ishaya 22:6-14
6
Elam ya ɗauki kwari da baka, tare da mahayan kekunan yaƙinta da dawakai; Kir ta buɗe garkuwoyi.
7
Kwarurukanku mafi kyau sun cika da kekunan yaƙi, an kuma tsai da mahayan dawakai a ƙofofin birni.
8
An rurrushe kāriyar Yahuda, a ranan nan kuwa kun yi la’akari da makamai a cikin Fadan Kurmi;
9
kuka ga cewa Birnin Dawuda tana da wuraren kāriya masu yawa da suka tsattsage; kuka tattara ruwa a Tafkin Ƙasa.
10
Kuka ƙirga gine-gine a Urushalima kuka kuma rurrushe gidaje don ku ƙarfafa katanga.
11
Kuka gina matarar ruwa tsakanin katanga biyu saboda ruwan Tsohon Tafki, amma ba ku yi la’akari da Wannan da ya yi su ba, ko ku kula da Wannan da ya shirya shi tuntuni.
12
Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki ya kira ku a wannan rana don ku yi kuka ku yi ihu, don ku aske gashinku ku kuma sa tsummoki.
13
Amma duba, sai ga shi kuna farin ciki kuna kuma murna, kuna yankan shanu kuna kashe tumaki, kuna cin nama kuna kuma shan ruwan inabi! Kuna cewa, “Bari mu ci mu kuma sha, gama gobe za mu mutu!”
14
Ubangiji Maɗaukaki ya bayyana wannan a kunnena cewa, “Har ranar mutuwarka ba za a yi kafarar wannan zunubi ba,” in ji mai girma Ubangiji Maɗaukaki.
Settings