Ishaya 22:1-11
1
Abin da Allah ya faɗa game da Kwarin Wahayi. Mene ne ya dame ku a yanzu, da dukanku kuka hau kan rufin gidaje.
2
Ya kai gari cike da hayaniya, Ya ke birnin tashin hankali da alkarya mai murna? Mutanenki ba su mutu ta wurin takobi ba, ba kuwa za su mutu a yaƙi ba.
3
Dukan shugabanninki sun gudu gaba ɗaya; an kama su ba tare da an yi amfani da baka ba. Dukanku da aka kama an kwashe ku ɗaurarru gaba ɗaya, kun gudu tun abokin gāba yana da nisa.
4
Saboda haka na ce, “Ƙyale ni kurum; bari in yi kuka mai zafi. Kada ka yi ƙoƙarin ta’azantar da ni a kan hallakar mutanena.”
5
Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana da ranar giggicewa da tattakewa da banrazana a cikin Kwarin Wahayi, ranar ragargazawar katanga da ta yin kuka ga duwatsu.
6
Elam ya ɗauki kwari da baka, tare da mahayan kekunan yaƙinta da dawakai; Kir ta buɗe garkuwoyi.
7
Kwarurukanku mafi kyau sun cika da kekunan yaƙi, an kuma tsai da mahayan dawakai a ƙofofin birni.
8
An rurrushe kāriyar Yahuda, a ranan nan kuwa kun yi la’akari da makamai a cikin Fadan Kurmi;
9
kuka ga cewa Birnin Dawuda tana da wuraren kāriya masu yawa da suka tsattsage; kuka tattara ruwa a Tafkin Ƙasa.
10
Kuka ƙirga gine-gine a Urushalima kuka kuma rurrushe gidaje don ku ƙarfafa katanga.
11
Kuka gina matarar ruwa tsakanin katanga biyu saboda ruwan Tsohon Tafki, amma ba ku yi la’akari da Wannan da ya yi su ba, ko ku kula da Wannan da ya shirya shi tuntuni.
Settings