Skip to content
Ishaya 13:6-16

Ishaya 13:6-16

6
Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki.
7
Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.
8
Tsoro zai kama su, zafi da azaba za su ci ƙarfinsu; za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu a ɓace.
9
Duba, ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana, mai hasala da zafin fushi, don ta mai da ƙasar kango ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta.
10
Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba.
11
Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
12
Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa, fiye da zinariyar Ofir wuyan gani.
13
Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki; duniya kuma za tă girgiza daga inda take a fushin Ubangiji Maɗaukaki, a ranar fushinsa mai ƙuna.
14
Kamar barewar da ake farautarta kamar tumaki marasa makiyayi, haka nan kowane mutum zai koma ga mutanensa, kowane mutum zai gudu zuwa ƙasarsa.
15
Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu; dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.
16
Za a fyaɗa ’ya’yansu a ƙasa su yi kucu-kucu a idanunsu; za a washe gidajensu, a kuma kwana da matansu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options