Hosiya 2:14-23
14
“Saboda haka yanzu zan rarrashe ta; zan bishe ta zuwa hamada in kuma yi mata magana a hankali.
15
A can zan mayar mata da gonakin inabinta, zan kuma sa Kwarin Akor yă zama ƙofar bege. A can za tă rera kamar a kwanakin ƙuruciyarta, kamar a lokacin da ta fita daga Masar.
16
“A waccan rana,” in ji Ubangiji, “za ki ce da ni ‘mijina’; ba za ki ƙara ce ni ‘maigidana’ ba.
17
Zan cire sunayen Ba’al daga leɓunanta; ba za a ƙara kira sunayensu ba.
18
A waccan rana zan yi alkawari dominsu da namun jeji da kuma tsuntsayen sararin sama da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa. Baka da takobi da yaƙi zan sa su ƙare a ƙasar, domin duk su zauna lafiya.
19
Zan ɗaura aure da ke har abada; zan ɗaura aure da yake cikin adalci da gaskiya, cikin ƙauna da jinƙai.
20
Zan ɗaura aure da yake cikin aminci za ki kuwa yarda cewa ni ne Ubangiji.
21
“A waccan rana zan amsa,” in ji Ubangiji, “zan amsa wa sararin sama, za su kuwa amsa wa ƙasa;
22
ƙasa kuma za tă amsa wa hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai, su kuma za su amsa wa Yezireyel.
23
Zan dasa ta wa kaina a ƙasar; zan shuka ƙaunata ga wanda na ce ‘Ba ƙaunatacciyata ba.’ Zan faɗa wa waɗanda a ce ‘Ba mutanena ba,’ ‘Ku mutanena ne’; za su kuwa ce, ‘Kai ne Allahna.’ ”
Settings