Hosiya 10:11-13
11
Efraim horarriyar karsana ce mai son sussuka; saboda haka zan sa karkiya a kyakkyawan wuyanta. Zan bi da Efraim, Dole Yahuda yă yi noma, dole kuma Yaƙub yă ja garman noma.
12
Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa, ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba; gama lokaci ne na neman Ubangiji, sai ya zo ya zubo adalci a kanku.
13
Amma kun shuka mugunta, kuka girbe mugu kuka ci ’ya’yan ruɗu. Domin kun dogara da ƙarfinku da kuma a jarumawanku masu yawa,
Settings