Skip to content
Hosiya 1:2-9

Hosiya 1:2-9

2
Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.”
3
Saboda haka sai ya auri Gomer ’yar Dibilayim, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa namiji.
4
Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila.
5
A wannan rana zan karye ƙarfin Isra’ila a Kwarin Yezireyel.”
6
Gomer ta sāke ɗauki ciki ta kuma haifi ’ya mace. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba ta suna, Lo-Ruhama, gama ba zan ƙara nuna wa gidan Isra’ila ƙauna ba, har da zan gafarta musu.
7
Duk da haka zan nuna ƙauna ga gidan Yahuda; zan kuma cece su, ba da baka, takobi ko yaƙi ba, ko ta wurin dawakai, ko masu hawan dawakai ba, sai ko ta wurin Ubangiji Allahnsu.”
8
Bayan ta yaye Lo-Ruhama, sai Gomer ta sāke haifi wani ɗa namiji.
9
Sai Ubangiji ya ce, “Ka ba shi suna Lo-Ammi, gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options