Farawa 50:7-11
7
Saboda haka Yusuf ya haura don yă binne mahaifinsa. Dukan hafsoshin Fir’auna suka yi masa rakiya tare da manyan mutanen gidan Fir’auna, da kuma dukan manyan mutanen Masar
8
da kuma dukan membobin gidan Yusuf, da ’yan’uwansa da kuma waɗanda suke na gidan mahaifinsa. Yara kaɗai da garkunansu da kuma shanunsu ne aka bari a Goshen.
9
Kekunan yaƙi da mahayan dawakai su ma suka haura tare da shi. Babbar ƙungiya jama’a ce ƙwarai.
10
Sa’ad da suka kai masussukar Atad, kusa da Urdun, sai suka yi kuka da ƙarfi da kuma mai zafi, a can Yusuf ya yi makoki kwana bakwai saboda mahaifinsa.
11
Sa’ad da Kan’aniyawa waɗanda suke zama a can suka ga makokin a masussukan Atad, sai suka ce, “Masarawa suna bikin makoki na musamman.” Shi ya sa ake kira wannan wurin da yake kusa da Urdun, Abel-Mizrayim.
Settings