Skip to content
Farawa 47:26-30

Farawa 47:26-30

26
Ta haka Yusuf ya kafa wannan ya zama doka game da ƙasa a Masar, har yă zuwa yau cewa kashi ɗaya bisa biyar na amfani gona ya zama na Fir’auna. Gonakin firistoci ne kaɗai ba su zama na Fir’auna ba.
27
To, Isra’ilawa suka zauna a Masar a yankin Goshen. Suka mallaki filaye a can, suka riɓaɓɓanya suka ƙaru ƙwarai.
28
Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai.
29
Sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, sai ya kira ɗansa Yusuf, ya ce masa, “Ka yi mini wannan alheri, ka sa hannunka ƙarƙashin cinyar ƙafata, ka yi mini alkawari saboda ina roƙonka kaɗa ka bizne ni a Masar,
30
amma sa’ad da na huta da kakannina, ka ɗauke ni, ka fid da ni daga Masar, ka binne ni a inda aka binne su.” Yusuf ya ce, “Zan yi yadda ka faɗa.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options