Farawa 39:4-7
4
sai Yusuf ya sami tagomashi a idanunsa, ya kuma zama mai hidimarsa. Fotifar ya sa shi yă zama shugaba a gidansa, ya kuma danƙa masa kome da yake da shi.
5
Daga lokacin da ya sa shi shugaban gidansa da kuma a kan dukan abin da yake da shi, sai Ubangiji ya albarkaci gidan mutumin Masar saboda Yusuf. Albarkar Ubangiji tana a kan kome da Fotifar yake da shi a gida da kuma a jeji.
6
Saboda haka sai ya bar kome a ƙarƙashin kulawar Yusuf, bai dame kansa a wani abu ba sai dai abincin da yake ci. To, fa, Yusuf ƙaƙƙarfa ne, kyakkyawa kuma,
7
bayan an ɗan jima sai matar maigidansa ta fara sha’awar Yusuf, sai ta ce, “Zo ka kwana da ni!”
Settings