An saka Yusufu a kurkuku ya sami albarka
19
Sa’ad da maigidansa ya ji labarin da matarsa ta faɗa masa cewa, “Ga yadda bawanka ya yi da ni,” sai ya husata.
20
Maigidan Yusuf ya ɗauke shi ya sa a kurkuku, wurin da ake tsare ’yan kurkukun sarki. Amma yayinda Yusuf yake can a cikin kurkuku,
21
Ubangiji ya kasance tare da shi; ya nuna masa alheri, ya kuma sa ya sami tagomashi a idanun mai gadin kurkukun.
22
Saboda haka mai gadin ya sa Yusuf ya zama shugaban dukan waɗanda aka tsare a kurkukun, Yusuf ne kuma yake lura da dukan abin da ake yi a can.
23
Mai gadin ba ya sa kansa game da kome da yake ƙarƙashin kulawar Yusuf, gama Ubangiji yana tare da Yusuf, ya kuma ba shi nasara a cikin dukan abin da ya yi.
Settings