Skip to content
Farawa 33:1-6

Farawa 33:1-6

1
Yaƙub ya ɗaga ido ke nan, sai ga Isuwa yana zuwa tare da mutanensa ɗari huɗu; saboda haka sai ya rarraba ’ya’yan wa Liyatu, Rahila da kuma matan nan biyu masu hidima.
2
Ya sa matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansu a gaba, Liyatu da ’ya’yanta biye, sa’an nan Rahila da Yusuf a baya.
3
Shi kansa ya sha gabansu, ya rusuna har ƙasa sau bakwai, kafin ya kai kusa da inda ɗan’uwansa Isuwa yake.
4
Amma Isuwa ya ruga a guje ya sadu da Yaƙub ya rungume shi; ya faɗa a wuyansa ya sumbace shi. Suka kuma yi kuka.
5
Sa’an nan Isuwa ya ɗaga ido ya ga mata da ’ya’ya. Ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan tare da kai?” Yaƙub ya amsa, “Su ne ’ya’yan da Allah cikin alheri ya ba bawanka.”
6
Sai matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansu suka matso kusa suka durƙusa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options