Skip to content
Farawa 33:5-11

Farawa 33:5-11

5
Sa’an nan Isuwa ya ɗaga ido ya ga mata da ’ya’ya. Ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan tare da kai?” Yaƙub ya amsa, “Su ne ’ya’yan da Allah cikin alheri ya ba bawanka.”
6
Sai matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansu suka matso kusa suka durƙusa.
7
Biye da su, Liyatu da ’ya’yanta suka zo suka rusuna. A ƙarshe duka, sai Yusuf da Rahila suka zo, su ma suka rusuna.
8
Isuwa ya yi tambaya, “Me kake nufi da dukan abubuwan nan da na sadu da su ana korarsu?” Sai Yaƙub ya ce, “Don in sami tagomashi a idanunka ne, ranka yă daɗe.”
9
Amma Isuwa ya ce, “Na riga na sami abin da ya ishe ni, ɗan’uwana. Riƙe abin da kake da shi don kanka.”
10
Sai Yaƙub ya ce, “A’a, ina roƙonka, in na sami tagomashi a idanunka, sai ka karɓi wannan kyautai daga gare ni. Gama ganin fuskarka kamar ganin fuskar Allah ne, yanzu da ka karɓe ni da farin ciki.
11
Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options