Farawa 18:1-15
1
Ubangiji ya bayyana ga Ibrahim kusa da manyan itatuwan Mamre yayinda yake zaune a mashigin tentinsa da tsakar rana.
2
Da Ibrahim ya ɗaga ido, sai ya ga mutum uku suna tsaye kusa da shi. Sa’ad da ya gan su, sai ya tashi nan da nan daga mashigin tentinsa, ya tarye su, ya rusuna har ƙasa.
3
Ya ce, “Ranka yă daɗe, in na sami tagomashi daga gare ku kada ku wuce bawanku.
4
Bari a kawo ruwa ku wanke ƙafafunku, ku huta a ƙarƙashin wannan itace.
5
Bari in samo muku wani abu ku ci don ku wartsake, sa’an nan ku ci gaba da tafiyarku; da yake kun biyo wurin bawanku.” Suka ce, “To, sai ka yi abin da ka ce.”
6
Saboda haka Ibrahim ya ruga zuwa wurin Saratu a cikin tenti ya ce, “Yi sauri, ki shirya mudu uku na gari mai laushi, ki cuɗa shi, ki yi burodi.”
7
Sa’an nan Ibrahim ya yi gudu zuwa garkensa, ya zaɓi ɗan maraƙi ya ba wa bawansa, bawansa kuma ya yi sauri ya gyara shi.
8
Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.
9
Sai suka ce masa, “Ina Saratu matarka?” Ibrahim ya ce, “Tana can cikin tenti.”
10
Sa’an nan ɗayansu ya ce, “Lalle zan komo wurinka war haka shekara mai zuwa. Saratu matarka kuwa za tă haifi ɗa.” Saratu kuwa tana a bayansu tana ji daga mashigin tenti.
11
Ibrahim da Saratu dai sun riga sun tsufa sosai. Saratu kuma ta wuce shekarun haihuwa.
12
Saboda haka Saratu ta yi dariya da ta yi tunani a zuci tana cewa, “Bayan ƙarfina ya ƙare, maigidana kuma ya tsufa, yanzu zan sami wannan jin daɗi?”
13
Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’
14
Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa.”
15
Saratu ta ji tsoro, don haka sai ta yi ƙarya ta ce, “Ban yi dariya ba.” Ya ce, “A’a, kin yi dariya.”
Settings