Galatiyawa 1:11-24
11
Ina so ku sani ’yan’uwa, cewa bisharar da nake wa’azi, ba mutum ne ya ƙago ta ba.
12
Ban karɓe ta daga wurin wani mutum ba, ba a kuma koya mini ita ba, a maimako, na karɓe ta, ta wurin wahayi daga Yesu Kiristi ne.
13
Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta.
14
Na ci gaba a cikin Yahudanci fiye da yawancin Yahudawan da suke tsarana, na kuma yi ƙwazo ƙwarai ga bin al’adun kakannina.
15
Amma sa’ad da Allah, wanda ya keɓe ni daga mahaifa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi
16
yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba.
17
Ban kuma tafi Urushalima domin in ga waɗanda suka riga ni zaman manzanni ba, sai dai na hanzarta na tafi ƙasar Arabiya, daga baya sai na koma Damaskus.
18
Bayan shekara uku, sai na haura zuwa Urushalima domin in sadu da Bitrus, na kuwa zauna tare da shi kwana goma sha biyar.
19
Ban ga wani a ciki sauran manzanni ba, sai dai Yaƙub ɗan’uwan Ubangiji.
20
Ina tabbatar muku a gaban Allah cewa abin da nake rubuta muku ba ƙarya ba ne.
21
Daga baya sai na tafi Suriya da Silisiya.
22
Ikkilisiyoyin da suke cikin Kiristi da suke a Yahudiya ba su san ni ba tukuna.
23
Sun dai sami labari ne kawai cewa, “Mutumin da dā yake tsananta mana yanzu yana wa’azin bangaskiyar da dā ya yi ƙoƙari yă hallaka.”
24
Sai suka yabi Allah saboda ni.
Settings