Ezekiyel 47:1-4
1
Mutumin ya komo da ni zuwa mashigin haikalin, sai na kuwa ga ruwa yana malalowa daga ƙarƙashin madogarar ƙofar haikalin wajen gabas (gama haikalin yana fuskantar gabas). Ruwan yana malalowa daga ƙarƙashin gefen kudun haikalin, kudu da bagaden.
2
Sai ya fitar da ni ta ƙofar arewa ya kewaye da ni ta waje zuwa ƙofar da take waje mai fuskantar gabas, ruwan kuwa yana malalowa daga wajen kudu.
3
Yayinda mutumin ya yi wajen gabas da karan awo a hannunsa, sai ya auna kamu dubu ya kuma bi da ni ta ruwan da zurfinsa ya kama ni a idon ƙafa.
4
Ya auna wani kamu dubu ya kuma bi da ni a ruwan da zurfinsa ya kai ni gwiwa. Ya sāke auna kamu dubu ya kuma bi da ni a ruwan da zurfinsa kama ni a gindi.
Settings