Ezekiyel 46:19-24
19
Sa’an nan mutumin ya fitar da ni ta ƙofar shiga a gefen ƙofar zuwa tsarkakakkun ɗakuna waɗanda suke fuskantar arewa, waɗanda suke na firistoci, ya kuma nuna mini wani wuri daga can ƙurewar yamma.
20
Ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya don laifi, da hadaya don zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gari, domin kada su kai su a filin da yake waje, su tsarkake mutane.”
21
Sa’an nan ya kawo ni filin da yake waje ya kuma bi da ni kewaye da kusurwoyi huɗunsa, na kuma ga kowace kusurwa na wani fili.
22
A kusurwoyi huɗu na filin da yake waje akwai waɗansu filaye a haɗe, tsawonsu kamu arba’in fāɗinsu kuwa kamu talatin; kowane fili a kusurwoyi huɗun nan girmansu ɗaya ne.
23
Kewaye da cikin kowane filin huɗun nan akwai ginin dutse, da murhu da aka gina a kewaye a ƙarƙashin ginin.
24
Sai ya ce mini, “Waɗannan su ne ɗakunan dahuwa inda masu hidima a haikali za su dafa hadayun da jama’a.”
Settings