Skip to content
Ezekiyel 38:1-13

Ezekiyel 38:1-13

1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, ka fuskanci Gog, na ƙasar Magog, babban sarkin Meshek da Tubal; ka yi annabci a kansa
3
ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.
4
Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in fitar da kai tare da dukan sojojinka, dawakanka, mahayan dawakanka saye da makamai, da kuma jama’a mai girma masu riƙe da garkuwoyi manya da ƙanana, dukansu da takuba a zāre.
5
Farisa, Kush da Fut za su kasance tare da su, duka riƙe da garkuwoyi da hulunan kwano,
6
haka ma Gomer da dukan sojojinsa, da Bet Togarma daga can arewa tare da dukan sojojinsa, al’ummai masu yawa tare da kai.
7
“ ‘Ka shirya; ka kintsa, kai da dukan jama’arka da suka taru kewaye da kai, ka kuma zama mai ba su umarni.
8
Bayan kwanaki masu yawa za a kira ka. A shekaru masu zuwa za ka kai hari a ƙasar da ta farfaɗo daga yaƙi, wadda aka tattara mutanenta daga al’ummai masu yawa zuwa duwatsun Isra’ila, dā kango ne sosai. An fitar da su daga al’ummai, yanzu kuwa dukansu suna zama lafiya.
9
Kai da dukan sojojinka da kuma al’ummai masu yawa da suke tare da kai za ku haura, kuna cin gaba kamar hadari; za ku zama kamar girgijen da yake rufewa ƙasa.
10
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, tunani zai shiga cikin zuciyarka za ka kuma ƙirƙiro muguwar dabara.
11
Za ka ce, “Zan kai hari wa ƙasar da ƙauyukanta ba su da katanga; zan fāɗa wa mutanen da suke zamansu kurum cikin salama, dukansu suna zama babu katanga babu ƙofofi ko ƙyamare.
12
Zan washe in kwashe ganima in kuma juye hannuna gāba da kufai da aka sāke zaunar da mutanen da aka tattara daga al’ummai, masu yawan shanu da kayayyaki, masu zama a tsakiyar ƙasa.”
13
Sheba da Dedan da ’yan kasuwar Tarshish da dukan ƙauyukanta za su ce maka, “Ka zo ka kwashe ganima ne? Ka tattara jama’arka don ka yi waso, ka kuma kwashe azurfa da zinariya, ka kwashe shanu da kayayyaki ka kuma ƙwace ganima mai yawa?” ’
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options